Saudi ta harba makami mai linzami

BBC ta ce tana da shaidar cewa, Saudiyya ta sayo makami mai linzamin ne daga Buritaniya.

Asalin hoton, Getty

Bayanan hoto,

BBC ta ce tana da shaidar cewa, Saudiyya ta sayo makami mai linzamin ne daga Buritaniya.

Kafar yada labarai ta BBC ta ga wata sheda, dake nuna cewa dakarun kawance da Saudiyya ke jagoranta, sun yi amfani ne da makami mai linzami da aka kera a Burtaniya, lokacin da suka lalata wani kamfani na fararen hula a Yemen.

Mutumin da ya mallaki kamfanin, ya nuna wa wakilin BBC tarkacen makamin mai linzami, da ake gani kirar kasar Burtaniya ne.

Editan sashin Larabci na BBC ya ce ana ci gaba da nuna damuwa a Burtaniya, kan yadda ake amfani da makaman da Burtaniyan ta sayar wa Saudiya, wajen kashe fararen hula, da sunan yaki da 'yan tawaye a Yemen.

Gwamnatin Burtaniyan ta ce tana takatsantsan sosai kan abin da ya shafi sayar da makamanta ga wasu kasashe, saboda haka, bata tunanin an sabawa sharuddan da kasa.