Sojojin Syria sun kwace Palmyra

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Har zuwa ranar Lahadi ana jin karar harbe-harbe a gabashin garin duk da cewa na fattaki mayakan IS a birnin Palmyra.

Kafofin yada labarai na Syria sun bayar da labarin cewa an kwace birnin Palmyra mai tsoho tarihi daga hannu mayakan IS.

Wani mai magana da yawun rudunar sojojin kasar ya shaidawa gidan talbijin na Syria cewa an kwace Palmyra kuma shine dan ba, na ganin bayan IS.

Sojojin Syria na samun galaba a 'yan kwanakin nan tare da taimakon jiragen saman yakin Rasha.

Kungiyar IS ta kama tsohon birnin Palmyra na Hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da kayan Tarihi UNESCO, da kuma sabon garin a watan Mayu na shekara 2015.

Wata kungiya mai sa ido a kan hakkin bil adama a Syria, mai shalkwata a Landan, ta ce har yanzu ana jin karar harbe-harbe a gabashin garin, amma yawancin mayakan IS sun gudu.