Uganda: Iyaye za su sha dauri kan kin rigakafi

Hakkin mallakar hoto Reuters

A Uganda, an kafa dokar da ke cewa za a yi wa duk iyayen da basu yi wa yaran su rigakafi ba daurin watanni uku a kurkukun kasar.

Wannan sabon kudirin doka ya samu amincewar majalisar dokokin kasar ne a watan Disamba da ta gabata.

Ministan lafiyar kasar, Sarah Achieng ta shaida wa BBC cewa, dama can akwai dokar rigakafi da ke cewa dole ne kowanne yaro ya zamana yana da katin allurar rigakafi, kafin a dauke shi a makaranta.

Kungiyar lafiya ta duniya ta ce yara fiye da miliyan 10 ne da basu karasa shekara biyar ba, ke rasa rayukan su a kasashen Afrika duk shekarar, sanadiyyar rashin samun rigakafi akan lokaci.