An samu dan China da laifin leken asiri

Satar bayanan sirri Hakkin mallakar hoto thinkstock
Image caption An yankewa Mr Su hukuncin shekaru Biyar a gidan kaso.

An samu wani dan asalin kasar Sin da laifin yin kokarin satar bayanan sirri masu muhimmanci ga Sojojin Amurka.

Ana zargin Mr Su Bin mai shekaru 50 a cikin wata kungiyar masu kutse a Kwamfuta dan satar bayanan sirrin jiragen yakin Amurka, da jiragen dakon kaya da makamai.

A wata sanarwa da ma'aikatar shari'ar Amurka ta fitar, ta ce za a hukunta shi daidai da laifin da ya aikata.

A shekarar 2014 ne aka kama Mr Su mazaunin kasar China, a lokacin da yake aiki a wani kamfani a kasar Canada.

An yanke masa shekaru Biyar a gidan kaso da tarar dala 250,000.

Harwayau, ma'aikatar shari'ar Amurka ta zargi gwamnatin China da sayan bayanan sirrin da Mr Su da masu taimaka ma sa suka sato.