An cafke barawon kaset a Amurka

Mr James Meyers
Image caption Ba dai ayi cikakken bayanin dalilin da ya sa Mr Meyers ya ki maida Kaset din ba duk tsahon wannan lokacin.

An cafke wani mutum mazaunin Arewacin Carolina a Amurka saboda kin mai da Kaset din da ya aro shekaru goma sha hudu da suka gabata.

Mutumin mai suna James Meyers ya ce ya na zaune a cikin motarsa kawai sai ga jami'an tsaro suka ce an ba su takardar izinin kama shi.

A shekarar 2002 ne dai Mr Meyers ya je wani shagon bada hayar Kaset na J&J ya aro Kaset din barkwanci, kuma tuni aka rufe shagon.

An gurfanar da shi gaban kotu, amma tun kafin a fara shar'ar aka sallame shi, bayan ya biya tarar dala 200.