Zika; Mata za su jinkirta haihuwa a Amurka

Mace mai juna biyu Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Macen da aka samu da alamun kwayar cutar za ta jinkirta daukar ciki, har sai bayan makwanni 18.

Jami'an lafiya a Amurka sun sake fitar da sabbin hanyoyin fadakarwa da suka shafi masu juna biyu da cutar Zika.

Sun bada sha'awar matan da aka samu da alamomin cutar, su dakata har zuwa makwanni 18 kafin su dauki ciki.

Ya yin da Maza kuma aka ba su shawarar su kauracewa Jima'ai har na watanni 6 ko kuma su yi amfani da kwararon roba.

Cizon sauro ne dai ya ke yada cutar ta Zika, amma daga baya an gano ana iya yada cutar ta hanyar Jima'i.

Zika na kara yaduwa kamar wutar daji a Latin Amurka, da yankin Caribbean, haka kuma cutar na janyo nakasa ga jarrirai ta yin nakasu a kwakwalwar su.