Brussels:Filin jirgi na rufe zuwa Talata

Hakkin mallakar hoto PA

Hukumomin Belgium sun ce filin jirgin sama na Brussels zai ci gaba da kasancewa a rufe ga fasinjoji har zuwa ranar Talata.

Injiniyoyi za su yi nazarin lafiyar gine gine da naurori a filin jirgin saman a karon farko tun bayan harin kunar bakin waken da ya faru a wannan makon.

A halin da ake ciki dai ana ci gaba da yin tambayoyi a game da ko an dauki matakan da suka dace domin hana aukuwar harin wanda ya hallaka mutane 31.

Jaridar le Mond ta Fransa ta wallafa abin da ta kira bayanan tambayoyin da yan sanda suka yi wa mutumin da ake zargi da harin Paris Salah Abdelsalam.

Jaridar ta ce an nuna masa hotunan yan kunar bakin waken da suka kai hari filin jirgin saman amma ya musanta saninsu kuma mai binciken bai matsa masa ya yi karin bayani ba.