Sabon shugaban Benin zai rage wa'adin mulki

Patrice Talon sabon zababben shugaban jamhuriyar Benin
Image caption Patrice Talon sabon zababben shugaban jamhuriyar Benin

Sabon zababben shugaban kasar Jamhuriyar Benin Patrice Talon yace yana da niyyar rage wa'adin shugabancin kasar ya koma wa'adin mulki daya kacal na shekaru biyar.

Mr Talon wanda ya kada Firayi ministan kasar a zagaye na biyu na zaben da aka yi a makon da ya wuce, yace hakan zai taimaka wajen yakar abin da ya kira shagala a kan kujerar shugabanci.

Yace zai kuma rage yawan ministocin gwamnati da kimanin rabi zuwa adadin ministoci 16.

Shugaban kasar mai barin gado Thomas Boni Yayi zai sauka daga karagar mulki bayan wa'adi mulki sau biyu.

Wannan matakin ya saba da akidar wasu shugabannin Afirka wadanda a baya bayan nan suka sauya kundin tsarin mulkinsu domin tsawaita shugabancinsu.