Wutar kasuwar Sabon Gari ta cigaba da ci

Image caption Jami'an kashe gobara na iya bakin kokarin su na ganin sun kashe wutar da ke ta ci.

Rahotanni daga jihar Kanon dai na cewa har yanzu wuta na ci gaba da ci a kasuwar ta Sabon Gari.

Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi na II ya katse ziyarar da ya ke yi a kasashen wajen domin ya dawo gida saboda gobarar da ta tashi a kasuwar sabon gari da ke jihar tun a daren ranar Jumma'ar da ta gabata.

Image caption Har yanzu wutar na ci a wasu rumfunan kasuwar

A halin da ake ciki Gwamnatin jihar Kano ta kafa wani kwamiti don bada shawara ta gaggawa kan abinda ya kamata gwamnati ta yi wa 'yan kasuwar da bala'in gobarar ya afka musu.

Ga dai karin bayanin da wakilinmu a Kanon Yusuf Ibrahim Yakasai ya yiwa Yusuf Tijjani ta wayar tarho.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti