Kebbi: 'Yan Kasuwa sun tafka asara a gobara

Image caption Sarkin Gwandu Alhaji Muhammadu Iliyasu Bashar ya na jajantawa 'yan kasuwar a yayin da ya kai ziyara

A jihar Kebbin Najeriya ana can ana kokarin tantance yawan asarar da aka yi sakamakon mummunar gobara da ta tashi a babbar kasuwar da ke birnin kebbi, baban birnin jahar.

Gobarar dai ta tashi ne da tsakar daren ranar Juma'a kuma ta wayi gari Asabar tana ci inda ta lakume kadarori na miliyoyin Nairori.

A wata hira da BBC wani daga cikin 'yan kasuwar da gobarar ta shafa ya ce matakin da 'yan banga da ke gadin kasuwar suka dauka na hana masu aikin sa kai da sauran jama'a shiga cikin kasuwar don su taimaka na daga cikin dalilan da suka janyo yawan asarar da aka yi.

Rahotanni sun ce kusan kashi casa'in cikin dari na rumfunan da ke kasuwar sun kone sai dai babu asarar rayuka.