Najeriya za ta tantance 'yan kunar bakin wake na Kamaru

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption A shekarar 2014 ne aka sace yammatan sakadiren Chibok

Gwamnatin Najeriya za ta tura wasu iyaye daga arewa maso gabashin kasar zuwa kasar Kamaru domin su tantance ko 'yar kunar bakin waken da aka kama na daga cikin yammatan Chibok da aka sace.

Bayan an kama 'yar kunar bakin waken a ranar Jumma'ar da ta gabata a Kamaru, ta shaida wa masu bincike cewa ta na daya daga cikin yammatan makarantar sakadiren Chibok da aka sace a shekarar 2014.

An kuma tsare wata matar ma tare da ita waccan.

Kuma dukkannin su sun daura abubuwan fashewa a jikinsu.

A baya-bayan nan dai mayakan Boko Haram na amfani da mata wajen kai harin kunar bakin wake.