Bernie Sanders ya sake samun nasara a jihohi 2

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Bernie Sanders ya samu nasarar ne a jihohin Washington da Alaska

Dan takarar shugabancin kasa a Jam'iyyar Democrat Bernie Sanders ya samu nasara a wa su jihohi biyu yayin da yake kokarin cike tazarar da ke tsakanin sa da abokiyar takarar sa Hillary Clinton.

Sanata Sanders ya lashe zaben ne a Washington da kuma jihar Alaska, yayin da har yanzu ba'a sanar da sakamakon zaben ba a jihar Hawaii.

Ko da yake batun takarar jam'iyyar Republican shi ne ya mamaye kafafan sadarwa da kuma shafukan sada zumunta, a bangaren Democrats ma ana fafatawa.

Har yanzu Bernie Sanders na fuskantar kalubale daga wajen babbar abokiyar takararsa Mrs Clinton wadda ke kan gaba a yanzu a zaben fitar da gwani a jam'iyyar ta su.

Sai dai kuma Mr Sanders, ya ce yana ganin zai iya samun nasara, inda ya ke shaidawa magoya bayansa cewa yana ganin zai fi gogayya ko kuma samun nasara akan Donald Trump idan har shi ya kasance dan takatarar jam'iyyar Demcrtas din.

Bernie Sanders ya cigaba da cewa ya na fatan nasarorin da ya samu za su kara masa kwarin guiwa a zaben Winsconsin da za'a yi nan da kwanaki 10, sai dai kuma sai ya yi da gaske ya iya cike tazarar da ke tsakanin sa da Mrs Clinton.