Masu zanga zanga a Brussels sun yi arangama

Hakkin mallakar hoto Reuters

A Belgium an jibge yansanda masu yawa da kuma motoci masu feshin ruwan zafi a tsakiyar dandalin place de la Bourse a Brussels babban birnin kasar a wani mataki na shirin ko ta kwana.

Yansandan sun tarwatsa gungun wasu masu tsattsauran ra'ayin kishin kasa wadanda suka taru a dandalin su na gaiguwa irin ta 'yan Nazi tare kuma da tunkarar wasu mata muslmi wadanda suka je wurin domin jimamin mutanen da suka rasu a harin bam din da ya faru a makon da ya wuce.

Tun da farko sai da yansandan suka kai samame wasu wurare a fadin kasar a ci gaba da farautar maharan da suka tsere.

A cikin wata sanarwa ofishin masu gabatar da kara yace an tsare mutane tara kawo yanzu kuma ana ci gaba da yiwa wasu mutane hudu tambayoyi.