Facebook ya nemi gafara kan harin Lahore

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu amfani da Facebook za su iya aike wa abokan su da 'yan uwa cewa suna nan lafiya a lokacin rikici

Shafin sada zumunta da muhawara na Facebook ya roki gafara ga daukacin masu amfani da shafin a duniya da ya aike wa sakonni don shaida wa abokan su cewa suna lafiya bayan harin bam din da aka kai a birnin Lahore na kasar Pakistan.

Wata matsala da aka fuskanta ce ta yi sanadiyar tura sakonni ga ma'abota shafin wadanda ko kadan basa kusa da birnin na Pakistan.

Fiye da mutane 70 ne suka mutu ciki har da kananan yara 29 a wani harin kunar bakin wake da aka kai a birnin Lahore kusa da wani wurin wasanni daya cika da iyalai wadanda wasun su ke bikin Easter ranar Lahadi.

Shafin Facebook dai ya samar da wata dama ce ta yadda mutanen da wani bala'i ya rutsa da su, zasu iya aikewa abokan su da 'yan uwa cewa suna nan lafiya.

Masana harkokin sada zumunta dai sun ce jama'a da dama ne a duniya ke amfani da shafukan sada zumunta wajen sanya hotuna da aikewa da sakonni yayin da aka samu wani rikici.