Kebbi: Shaguna 1,700 ne suka kone — NEMA

Hakkin mallakar hoto Channels TV
Image caption Gobarar ta lakume kadarori na miliyoyin Nairori.

Kimanin shaguna da rumfunan kasuwa 1,700 ne suka kone kurmus a bala'in gobarar da aka yi a babbar kasuwar Birnin Kebbi.

Jami'in hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya mai kula da shiryar Sakkwato, Mr. Thickman Tanimu ne ya sanar da hakan bayan wata ziyara da tawagar hukumar ta kai kasuwar ranar Lahadi.

Ya ce ko da yake babu wanda ya rasa ransa ko ya samu rauni a cikin lamarin, akwai 'yan kasuwar da dama da aka kwantar a asibiti sakamakon halin kaduwa da suka shiga bayan ganin irin asarar da suka yi.

Gobarar dai ta tashi ne da tsakar daren ranar Juma'a kuma ta wayi gari Asabar tana ci inda ta lakume kadarori na miliyoyin Nairori.

A wata hira da BBC wani daga cikin 'yan kasuwar da gobarar ta shafa ya ce matakin da 'yan banga da ke gadin kasuwar suka dauka na hana masu aikin sa kai da sauran jama'a shiga cikin kasuwar domin su taimaka, na daga cikin dalilan da suka janyo yawan asarar da aka yi.

Sai dai rahotanni sun ce matsalar na'urar samar da wuta mai amfani da hasken rana na daga cikin dalilan da suka haddasa gobarar.