Mutane a kalla 50 sun mutu a Lahore

Hakkin mallakar hoto Reuters

A kalla mutane 50 sun mutu wasu da dama kuma sun jikkata yayin da bam ya fashe a wani wurin shakatawa a birnin Lahore a kasar Pakistan.

Yansanda sun ce wani dan kunar bakin wake ne ya tada da bama bamai kusa da wani wurin wasan yara inda iyalai da dama suka hadu.

Wani wanda ya shaidar da lamarin yace an sami rudani da turmutsitsi yayinda kowa ke neman tsira.

An garzaya da mutane da dama da suka hada da kananan yara zuwa asibiti.

Ba a san ko su wanene suka kai harin ba.