Mutane 70 sun mutu a harin Lahore

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mutane saba'in ne suka mutu a harin Lahore na kasar Pakistan

Fiye da mutane 70 ne suka mutu ciki har da kananan yara 29 a wani harin bam da aka kai a birnin Lahore na kasar Pakistan.

Wani dan kunar bakin wake ne dai ya tarwatsa kansa kusa da wani wurin wasanni da ya cika da iyalai wadanda wasun su ke bikin Easter ranar Lahadi.

Reshen kungiyar Taliban Jamaat-ul-Ahrar, da ya balle daga uwar kungiyar ne ya dauki alhakin kai harin.

Hukumomi dai sun ayyana zaman makoki na kwanaki uku yayin da Firai ministan kasar Nawaz Sharif, ya dage ziyarar da yake shirin kai wa zuwa Birtaniya.

Wani mai bai wa Firai ministan Pakistan shawara Tariq Fatimi, ya shaidawa BBC cewa ire-iren wadannan hare-hare ba su da wani amfani saboda suna shafar wadanda ba su ji ba su gani ba.