Jam'iyyu 3 sun goyi bayan Mahamadou Issoufou

Hakkin mallakar hoto
Image caption Jam'iyun sun ce akwai bukatar daukacin 'yan Nijar su hada kai don ciyar da kasar gaba.

A Jamhuriyar Nijar wasu jam'iyun siyasa da suka hada da MPR Jamhuriya da PSD Basira da kuma ARD Adalci-Mutunci sun jaddada goyon bayan su ga Shugaban kasar Mahamadou Issoufou da gwamnatin sa domin tafiyar da al'amurran kasar.

A wata sanarwa, Jam'iyun sun ce akwai bukatar daukacin 'yan Nijar su hada kawunan su don ciyar da kasar gaba.

Hakan dai na faruwa ne daidai lokacin da kawancen jam'iyun siyasa na adawa ya yi watsi da sakamakon zaben da aka yi a kwanakin baya.

A wata hira da BBC, Shugaban jam'iyar PSD Basira Honorable Ben Omar Mohamed ya ce daukacin 'yan Majalisun jam'iyyun uku na kira ga saura jam'iyyun adawa da su yi hakuri da yadda sakamakon zabe ya kasance don ciyar da Nijar gaba.