Brussels: Jami'ai sun saki Faycal C.

Hakkin mallakar hoto Belgian Fed Police
Image caption Hoton bidiyo ya nuna Faycal C. tare da wasu da ake zargi sunyi kunar bakin waken da ya afku a Brussels.

Babban mai shigar da kara a Brussels, ya ce, an saki wani mutumi da ake zargi da alaka da harin da aka kai birnin, sakamakon rashin samun sa da laifi.

Jami'ai dai sun sanar da Faycal C, a matsayin sunan sa.

Da farko wasu da ke aiki tare da masu bincike sun ce sunansa Faycal Cheffou, wanda a da ake zargi da ayyukan ta'addanci, har ma da kisa.

Wasu kafofin yada labarai ma sun ce kamarsa ta so ta zo daya da wani da hoton bidiyon filin jiragen ya dauka, inda aka hango shi tare da wasu maza biyu, da ake zargin sun yi kunar bakin wake.

Ministan lafiya na Belgium, ya ce wasu karin mutane hudu da suka jikata a harin da aka kai ranar Talata a Brussels sun mutu, wanda ya kai adadin wadanda suka mutu a harin zuwa 35.