Cameroon: 'Yan matan Chibok ne suka kai hari?

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ana samun bayanai daga wajen yammata 'yan kunar bakin waken da aka kama a Kamaru

Har yanzu gwamnatin Kamaru ba ta tabbatar da cewa ko daya daga cikin 'yan matan da aka kama a Limani' bisa zargin kai harin kunar bakin wake, na daga cikin 'yan matan Chibok ba.

Rahotanni dai sun bayyana cewa ana ci gaba da tatsar bayanai daga gare su duk da cewa daya daga cikin matan na kwance a asibiti.

Tuni gwamnatin Najeriya ta ce za ta tura wasu iyaye daga arewa maso gabashin kasar, zuwa kasar Kamaru domin su tantance ko 'yar kunar bakin waken da aka kama na daga cikin 'yammatan Chibok da aka sace.

Wakilin BBC na Kamaru, Mohaman Babalala ya tattauna da daya daga cikin shugabannin 'yan kato da gora na garin Limani' domin jin yadda suka kama wadannan 'yan mata.

Ga kuma yadda tattaunawar tasu ta kasance;

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti