Harin Ivory Coast: An kama mutane biyu

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption jami'an tsaro na cote d'ivoire

Sakamakon harin da aka kai a kasar Cote-d'ivoire, jami'an tsaro sun kama mutane 2 a arewacin Mali.

Ana zargin mutanen da hannun cikin harin Grand Bassam wanda ya hallaka mutane 19 a ranar 13 ga watan Maris 2016.

An ce mutumin farko da aka kama a yankin Tombouctou shi ne ya tsara kai harin.

Dayan kuma da aka kama a yankin Gao, na hannun daman Kounta Dalla ne, wato jagoran ayarin maharan.