Sojojin Nigeria sun kai samame a Falgore

Dajin Falgore, inda masu satar shanu ke addabar makiyaya.
Bayanan hoto,

Dajin Falgore, inda masu satar shanu ke addabar makiyaya.

A Najeriya, a yayin da matsalar satar shanu da garkuwa da mutane ke kara ta'azzara a wasu jihohin arewacin kasar, dakarun rundunar sojin kasar suna gudanar da wani samame a dajin Falgore dake jihar Kano.

Bayanai sun nuna cewa dajin na Falgore ya zama wani matattara na masu gudanar da mugunyar sana'ar, satar shanu.

Rahotanni sun ce sojojin sun danna cikin dajin na Falgore ne domin fatattakar barayin shanun da masu garkuwa da mutane da suka addabi Kano, dama wasu jihohin dake makwaftaka da ita.

A ranar Asabar da ta gabata ma, sai da wasu da ake zargi masu garkuwa da mutane ne suka sace wani soja mai mukamin Kanar a Kaduna, yayin da a can baya kuma, aka sace mahaifiyar wani dan majalisar dokoki a jihar ta Kano, wacce aka sako daga baya.

A baya dai rundunar 'yan sandan jihar Kanon tace jami'anta sun kashe wasu mutane takwas da ake zargi da satar shanu yayin wata mummunar musayar wuta da barayin a dajin na Falgore.

Matsalar satar shanu na daga cikin matsalolin da ake fuskanta ta fannin tsaro a arewacin Najeriya, hakan kuma na jawo asarar rayuka da dukiyoyi.