Shin ka san irin barnar da gobara ta yi a kasuwar Kano?

A ranar Juma'a da tsakar dare, yayin da al'ummar jihar Kano a arewacin Najeriya ke tsaka da bacci kamar yadda kowanne bil'adama ke yi a wannan lokacin, a kasuwar Muhammadu Abubakar Rimi kuwa da aka fi sani da kasuwar Sabon Gari, lokacin ne gobara take ci ba kakkautawa.

Gobarar dai ta fara ci ne tun karfe 12 na tsakar daren Juma'ar.

Rahotanni sun ce wannan gobara ta ci gaba da ci har zuwa wayewar gari amma ba a samu nasarar kasheta ba sakamakon tashin da ta yi cikin dare yadda babu wani agajin gaggawa da aka kai a lokacin har sai da gari ya waye aka fara kokarin kasheta.

Wannan mummunar gobara dai ta tsayar da tafiyar al'amura da yawa a birnin Dabon, kuma har bayan kwanaki uku da faruwar lamarin ba a kai ga sanin musabbabinta ba.

An shafe sama da sa'o'i 20 ana kokarin shawo kan gobarar amma ba ta mutu gaba daya ba har sai wayerwar garin Lahadi.

"Kokarin kashe gobarar"

Za a iya cewa daukacin motocin kashe gobara da ke jihar Kano ne suka dinga kai kawo a yunkurin kashe gobara mafi muni a tarihin kasuwannin Kano.

Motocin kashe gobara na gwamnati da na masana'antu masu zaman kansu sun yi ta ci gaba da yunkurin kashe gobrar.

A lokacin da gobarar ke ci gaba da ci, Kwamishinan ciniki da masana'antu na jihar Kano Alhaji Rabiu Bako, ya shaida wa gidan radiyon jihar cewa ana yunkurin samar da jiragen sama masu saukar ungulu domin kashe gobarar, amma har ta ci ta cinye ba a ga wadannan jirage ba.

Ita ma rundunar 'yan sandan jihar Kano ta tura sama da jami'anta 500 domin samar da tsaro a kasuwar Sabon Gari a daidai lokacin da wutar ke ci.

"'Yan gani da ido"Wani da ke tsaro a kasuwar ta Sabon Gari wanda kuma yake wajen lokacin da gobarar ta fara tun cikin daren, ya shaida wa BBC cewa, "Muna hirar dare a bakin titin Murtala Muhammad Way kusa da Sabon Gari sai muka hango wuta ta fara dagawa daga cikin kasuwar, ko kafin mu karasa wajen tuni wutar ta wuce tunaninmu."

Shi ma wani da yake da shago a kasuwar ga abinda ya shaida wa wakilin BBC, "Tsakanin inda nake da inda wutar take ci ya kai tafiyar rabin kilomita, amma cikin sa'a guda sai ga wutar har ta kawo inda nake. Mu dai mun zubawa sarautar Allah ido ne kawai domin wutar ta fi karfinmu, idan an tare nan sai ka ga ta bullo ta can."

Mutumin ya kara da cewa, "Haka muna ji muna gani dukiyarmu ta kone kurmus. Ni dai duk abin da ke cikin rumfata to ya salwanta."

Sarkin kasuwar ta Sabon Gari Alhaji Nafi'u Nuhu Indabo, wanda shi ma runfarsa ta kone ya yi karin bayani kan gobarar.

Ya ce, "Fiye da rabin kasuwar ya kone, a iya cewa kashi 75 cikin 100, kuma a tsakiyar kasuwa wannan barna ta fi yawa. Akwai shagunan inyamurai da basa nan sun tafi hutun Easter wanda an yi kokarin balle shagunan don a tserar da kayan ciki kafin gobarar ta kai garesu amma ba halin yin hakan tunda masu shagunan ba sa nan."

"Mafarin gobarar"

Wannan gobara dai ta fara ne daga layin 'yan takalma, inda daga nan kuma ta dinga bi layi-layi da sako-sako tana kama ragowar shaguna tana lamushe su.

Layunka da suka kone sun hada da block A da B da C da D da kuma L, inda suka hada har da shahararrun layuka kamar na 'yan magunguna da layin masu kayan kicin da na 'yan littatafai da sauransu.

"Rashin madafa"

Rahotanni sun ce dubban mutane ne suka yi cincirindo a bakin manyan kofofin shiga kasuwar ba tare da sanin abin yi ba, sakamakon yadda hayaki ya turnuke sararin samaniyar yankin, har ma wadanda suke unguwanni nesa da kasuwar na iya hango bakin hayakin mai kama da bakin hadari.

Amma duk da haka a wasu bangarorin da wutar bata gama kai wa ba, an samu wadanda suka yi shahadar kuda suka kutsa layin shagunansu don kwaso ko dai kaya ko kuma farin kudi da su kan ajiye.

Gidajen radiyon da ke Kano sun gudanar da shirye-shirye na kai tsaye kan gobarar don bai wa al'ummar jihar damar sanin me yake faruwa.

"Gobara mafi muni"

Hukumar bayar da agajin gayawa ta Nigeria NEMA, ta ce sama da shaguna 3,800 ne suka kone a gobarar da aka yi a kasuwar Sabon Gari da ke jihar Kano a arewacin Nigeria.

Shugaban hukumar ta NEMA Alhaji Sani Sidi, ya shaida wa BBC cewa gobarar ta Sabon Gari ita ce mafi muni da aka taba yi a wata kasuwa a Najeriya.

Alhaji Sani Sidi ya ce mutane 15 ne suka jikkata a gobarar, sannan babu asarar rayuka.

Shugaban ya ce kawo yanzu ba a kai ga kididdige irin dukiyar da aka rasa ba a gobarar.

Sai dai kungiyar 'yan kasuwa ta jihar Kano ta shaida wa wasu kafofin yada labarai cewa, a kalla asarar da aka yi za ta iya kai wa ta naira tiriliyan biyu.

Ta kuma ce wannan asara ta shafi a kalla mutane 18,000.

A nata bangaren, rundunar 'yan sandan jihar Kano tace an kama sama da mutane 100 da ake zarginsu da sace-sace a yayin da gobarar ke ci.

Sarkin kasuwa Nuhu Indabo ya ce, "Wallahi bamu taba ganin bala'i mafi muni da ya samu jihar Kano irin wannan ba."

"Rashin Tsari"

Mutane da dama sun dora alhakin yawan barnar da wutar ta yi a kasuwar kan rashin tsari da ake da shi a kasuwanni.

Kazalika, tsarin da wasu 'yan kasuwar ke dashi na ajiyar tsabar kudi a cikin shago ba tare da kai su banki ba ya kara yawan asarar.

Nuhu Indabo ya ce dole ne sai 'yan kasuwa sun sauya tsarin shagunansu inda suke baza kaya har bakin shago su tare hanya in har ana son dakatar da munin gobarar irin wannan.

A wani mataki na nuna alhini kan gobarar ta Sabon Gari, kungiyar 'yan kasuwar kwanar Singer da ke makwabtaka da Sabon Garin ta ce ta nemi 'yan kasuwarta da kada su bude shaguna ko kasa kaya.

Mataimakin shugaban riko na kasuwar ya shaida wa BBC cewa sun dauki matakin ne domin jajantawa takwarorin nasu da kuma nuna alhini kan abin da ya shafe su.

"Kokarin gwamnati"

Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ta kafa wani kwamiti domin bayar da shawara ta gaggawa kan abinda ya kamata gwamnati ta yi wa 'yan kasuwar da bala'in gobarar ya afka musu.

Kafa kwamitin dai na zuwa ne a daidai lokacin da 'yan kasuwar ke kokarin tantance irin asarar da suka tafka sakamakon gobarar, wacce ta fara tun tsakar daren juma'a ta kuma shafe wunin Asabar tana ci gaba da kone shaguna, inda sai wayewar garin Lahadi ne ta gama mutuwa baki daya.

Shima Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II, ya shawarci 'yan kasuwa da su rinka kai kudadensu ajiya bankuna maimakon barin su a shaguna, a wani mataki na rage yawan asara a lokacin gobara.

Sarkin wanda ya katse ziyarar da yake a kasahen waje ya koma gida, ya yi kira ga hukumomi a matakin jiha da gwamnatin tarayya da su tsananta bincike domin gano musabbanin abinda ke janyo afkuwar gobara musamman a kasuwanni.

A yanzu mafi yawan kasuwar dai ya zama toka, wanda hakan ke nuna cewa al'amuran kasuwanci sun samu mummunan koma baya, a lokacin da jama'a ke cikin halin ka-ka-ni-kayi.

Gobarar dai za ta mayar da daruruwan mutanen da suke daukar nauyin wasu, su zama suma masu neman a taimaka musu da abinda za su yi bukatun yau da kullum, za kuma a kara samun marasa ayyukan yi da za su zurawa gwamnati ido domin samar musu abin yi, domin kuwa da dama daga 'yan kasuwar a yanzu ba su da makama, ba su da tudun dafawa, don haka ba su ma san me za su yi ba, ko ma ta ina za su fara.

An sha samun gobara a kasuwannin jihar Kano da suka hada da sabon gari da kwari da Singer da kuma Kurmi, amma wannan ce mafi muni.