Damuwa kan amfani da hanyoyin sada zumunta

Hakkin mallakar hoto
Image caption Akasarin daliban da ke aike wa da sakonni batsa shekarun su ba su wuce 13 zuwa 16 ba.

Wani bincike da aka gudanar ya nuna cewa akasarin malamai suna sane da cewa wasu daga cikin daliban su na aike wa da hotona da bidiyo na batsa ta hanyoyin sada zumunta na zamani.

Sakamakon binciken da kungiyar malamai ta gudanar ya nuna ce wa kimanin malamai 1,304 da aka nemi jin ra'ayoyin su, sun ce akasarin dalibai da ake samu suna aika irin wadannan sakonni shekarun su ba su wuce 13 zuwa 16 ba, inda a wa su lokutan ma akan samu masu shekaru 7.

Binciken na zuwa ne yayin da jam'iyyar Labour ta zargi gwamnati da kin kare al'ummar wannan zamani da ke amfani da wayoyin tafi da gidan ka na smartphone.

Kazalika binciken da aka gudanar game da rashin bin ka'ida wajen amfani da hanyoyin sada zumunta, ya gano cewa kusan rabin malamai sun fuskanci kalamai na batanci da wa su dalibai ko iyaye ke yi akan su.