An kashe babban sojan Najeriya da aka sace

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rundunar ta bayyana rashin jin dadinta game da lamarin, inda ta sha alwashin hukunta duk wadanda ke da alhakin wannan mummunan aiki.

Rundunar sojojin Najeriya ta sanar da cewa ta gano gawar babban hafsanta da aka sace a Kaduna.

Wata sanarwa da ta fito daga rundunar sojojin ta ce an gano gawar Kanar Samaila Inusa ne ranar Talatar nan da misalin karfe 6 na yamma.

Sanarwar ta sojoji dauke da sa hannun Kanar Sanu Usman Kukasheka ta ce binciken da aka gudanar na farko-farko ya nuna alamun cewa an kashe babban hafsan sojan ne, ranar da aka sace shi, ganin yadda gawar ta soma rubewa a kauyen Ajyaita da ke gabashin jihar Kaduna, a inda aka tsinto ta.

Sanarwar ta ce an soma shirye-shiryen kai gawar asibitin rundunar, mai suna 44 Nigerian Army Reference Hospital da ke Kaduna.

Rundunar ta kara da cewa, tana son sanar da al'ummar kasar cewa za ta tsananta bincike kan wadanda ke da alhakin wannan mummunan aiki, kuma dole a yi masu tsattsauran hukuncin da doka ta tanadar.

Wasu wadanda ba a kai ga tantance ko su wanene ba ne suka sace hafsan sojan ranar Lahadi 27 ga watan Maris, inda suka sauke matarsa daga cikin motar sa, suka yi awon gaba da shi da motar.