Brazil: Shin za a tsige Dilma Roussef?

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Dilma Roussef ta shigar da kara kan bata mata suna da ta ce an yi kan badakalar kamfanin mai na Petrobras.

Gwamnatin hadaka ta Brazil ta samu babban koma baya, bayan janyewar babbar jam'iyyarta.

Janyewar jam'iyyar PMDB ya tayar da fargabar cewa za'a iya tsige shugaba Dilma Rousseff.

Shugabar kasar ta shiga wata hatsaniya da ta hada da kamfanin mai na kasar, watau Petrobas, inda ake zarginta da rufa-rufa kan bayanan kudadan kasar, domin boye matsanancin halin da tattalin arzukin Brazil din ya shiga.

Rahotannin sun ce ranar Alhamis ministan kudi, Nelson Barbosa, zai bayar da shaida ga kwamitin Majalisar Dokoki, kan tsige shugabar kasar.

Tsohon shugaban jam'iyyar ta ta Workers' Party a Majalisar dattawa, Delcidio Amaral,ya shaida wa wata mujalla cewa Ms Rousseff na da masaniyar cewa ana karkatar da kudade a Petrobras, kuma ta yi yunkurin hana bincike a kan badakalar.

Sai dai kuma fadar shugaban kasar ta musanta zarge-zargen, amma kuma ana ci gaba da samun karuwar matsin lamba a kan a fara daukar matakin tsige Ms Rousseff daga kan mukamin ta.

Shi ma dai tsohon shugaban kasar Luis Inacio Lula da Silva na fuskantar tuhuma na amundahana a kamfanin mai na Petrobras.