Za a rantsar da sabon shugaban CAR

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Za a rantsar da sabon shugaban Jamhuriyar tsakiyar Afrika

A ranar Laraba ne za a rantsar da zababben shugaban kasa a Jamhuriyar tsakiyar Afirka Faustin-Archange Touadéra.

'Yan kasar dai na cike da fatan cewa sabon shugaban zai dauki kwararan matakai don kawo karshen shekaru 3 da aka kwashe ana ta yake-yake na kabilanci da kuma na addini.

A jajiberin wannan biki kuma, Shugabar kasar mai barin gado Cathérine Samba Panza ta gabatar da irin ayyukan da ta yi na tsawon shekaru biyu a kan mulki, tare kuma da bayyana yadda take kallon makomar Jamhuriyar tsakiyar Afrikan.

Cathérine Samba Panza ta cigaba da cewa wanda zai gajeta na da babban kalubale a gabansa, inda ta ce talauci shi ne makasudun abinda ya haifar da tashe-tashen hankula a Jamhuriyar tsakiyar Afrika.