Ghana ta tasa keyar 'yan sandan Afrika Ta Kudu

Hakkin mallakar hoto Chris Stein AFP

Ghana ta mayar da wasu 'yan sandan Afrika Ta Kudu su uku da ta tsare gida, bayan sun shigo kasar a matsayin masu bayar da horo ga masu tsaron shugabannin jam'iyyun adawar kasar.

Daya daga cikin lauyoyin 'yan sandan uku, Nana Bediatuo Asante, ya shaida wa BBC cewa duk da cewa an zarge su da neman aikata muggan laifuka da bayar da horo ba bisa ka'ida ba, yanzu an soke zargin.

Kazalika Lauyan ya ce mayar dasu da gwamnatin Ghana ta yi ba zai bayar da damar ci gaba da karar ba.

Hukumomin shige da ficen kasar Ghana sun kwace takardun shigarsu kasar, inda aka sanya su shiga jirgin Afrika Ta Kudun da ke hanyar Johannesburg, babban birnin kasar.

Hukumar bincike ta kasa ta ce tsoffin 'yan sandan na bai wa matasa 15 horo ne kan ayyuka daban-daban da suka jibanci yaki, da iya fada da ma amfani da makami.

Ta kuma ce suna bayar da horon kan yadda zasu kare manyan mutane idan ta kama, da kuma kai daukin gaggawa idan abu ya faru.