Burkina Faso: Rikicin makiyaya da manoma yana kamari

Image caption Burkina Faso na iyaka da Ivory Coast da Ghana.

Jami'ai a Burkina Faso sun ce fiye da mutane dubu daya, akasari mata da kananan yara ne suka ketara zuwa Ivory Coast, sakamakon rikici tsakanin makiyaya da manoma, a Bouna da ke arewa maso gabashin kasar.

An ce jama'a na ci gaba da ketara wa zuwa yankin Noumbiel, inda suke fama da rashin kulawa.

Fiye da mutane dari biyu kuma sun ketara zuwa kasar Ghana.

Akalla mutane goma sha bakwai ne aka kashe yayin da wasu da dama suka samu raunuka a rikicin.

Rashin jituwa tsakanin makiyaya da manoma dai yana janyo asarar rayuka da dunkiyoyi, a kasashen Afirka ta yamma.