A ceto mutanen da BH ta sace a Damasak — HRW

Hakkin mallakar hoto
Image caption Kimanin mutane 400 mayakan Boko Haram suka sace a Damasak
Kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Rights Watch, ta yi kira ga gwamnatin Nigeria da ta dauki matakin gaggawa don ganin an ceto kimanin mata da yara 400 da kungiyar Boko Haram ta sace a garin Damasak shekara guda da ta gabata.

Kungiyar ta ce har yanzu ba ta tabbatar ko gwamnatin kasar ta yi wata hobbasa don ganin an saki mutanen wadanda suka hada da 'yan makaranta 300, a garin Damasak da ke jihar Borno ba.

Yaran makarantar Damasak sune mafi yawa da kungiyar Boko Haram ta taba sacewa, amma mutane basu mayar da hankali kan batun ba kamar yadda aka damu da sace 'yan matan makarantar Chibok da kungiyar ta yi a watan Afrilun 2014.

A sanarwar da Human Rights Watch ta fitar wata mai bincike a kungiyar Mausi Segun, ya ce, "An sace yara 300 tun shekara guda da ta gabata, amma har yanzu gwamnati ba ta ce komai ba."

Ta kara da cewa, "Don haka ya zama wajibi hukumomi su farka don gano inda yaran Damasak da sauran mutanen da aka sace suke don kubutar da su."

"Waiwaye"

A ranar 24 ga watan Nuwambar shekara ta 2014 ne mayakan Boko Haram suka kai hari garin Damasak da ke kusa da kan iyakar jamhuriyar Nijar, suka tare duk hanyoyin shiga garin.

Kungiyar Human Rights Watch ta ce a bayanan da ta samu an shaida mata cewa, mayakan sun mamaye makarantar Firamare ta Zanna Mobarti suka kulle kofofin tare da rufe yara kusan 300 masu shekaru tsakanin 7 zuwa 17 a ciki.

Daga bisani mayakan suka mayar da makarantar sansani inda suka dinga tara matan da suka kamo a cikin gari suka yi garkuwa da su.