Sankarau ta hallaka mutane 61 a Nijar

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kashi talatin cikin dari na wadanda suka kamu da cutar kananan yara ne 'yan kasa da shekaru biyar.

A Jamhuriyar Nijar kimanin mutane 61 ne suka mutu sakamakon bullar annobar cutar sankarau a wa su yankunan kasar.

Wani rahoto da hukumar samar da agajin gaggawa ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ya ce daga watan Janairu zuwa watan Maris na 2016, kimanin mutane 736 suka kamu da cutar.

Kashi talatin cikin dari na wadanda suka kamu da cutar kananan yara ne 'yan kasa da shekaru biyar, yayin da kashi talatin da biyar cikin dari masu shekaru goma sha hudu ne da haihuwa.

Sai dai ma'aikatar lafiya ta kasar ta na daukar matakan da suka dace don shawo kan cutar, inda ya zuwa yanzu aka yi wa mutane dubu dari da arba'in da daya allurar rigakafin cutar sankarau inda kuma aka yi odar wasu magungunan rigakafin.