BH: 'A taimaka a ceto yaranmu da aka sace'

Hakkin mallakar hoto
Image caption Iyayen sun bukaci gwamnati da ta gano tare da kubutar da mutanen da mayakan Boko Haram suka sace

A Najeriya, 'yan uwan mata da yara 400 ciki har da 'yan makaratar firamare 300 da kungiyar Boko Haram ta sace shekarar da ta gabata sun koka da abin da suka kira halin ko in kula da hukumomi ke nunawa kan batun.

A cewarsu ba a dauki wasu kwararan matakai ba wajen ganin cewar an gano inda mutanen da aka sace su ke.

Mutanen dai na tsokaci ne a kan rahoton da kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Rights Watch ta fitar wanda ke kira ga gwamnatin Najeriyar ta dauki mataki domin ganin an ceto rayukan mutanen da aka sace.

Wasu daga cikin 'yan uwan wadanda aka sace a garin na Damasak sun shaida wa BBC cewa, suna cikin wani mawuyacin hali na rashin sanin halin da 'yan uwan su ke ciki.

Sun kuma bukaci gwamnatin kasar da ta gaggauta daukar matakai don gano tare da kubutar da mutanen da mayakan Boko Haram suka sace.