Za mu kawo karshen karancin mai - Kachikwu

Ministan ma'aikatar mai ta Najeriya Dr Emmaneul Ibe Kachikwu, ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba za a kawo karshen karancin man da ake fama da shi a kasar.

Minista Kachikwu ya bayyana hakan ne ranar Talata, a lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin kula da harkokin man fetur na Majalisar dattawan kasar, domin ya amsa tambayoyi a kan matsalar karancin man fetur din da ake fuskanta a sassan kasar daban -daban.

Kachikwu ya kuma kara da cewa suna sane da cewa masu ababen hawa da kuma sauran al'umma na cikin matsi sakamakon wahalar man fetur din, a don haka ya yi alkawarin cewa lamura zasu sauya a cikin makwani kalilan masu zuwa.