Amurka ta janye shari'a da kamfanin iPhone

Hakkin mallakar hoto AFP Getty
Image caption Kamfani Apple ne kawai yake iya tono bayanan da ke kunshe a wayar iPhone.

Sashen shari'a na kasar Amurka ya janye shari'ar da yake yi da kamfanin waya na iPhone, bisa kin amincewar kamfanin na ya bude bayanan da wayar ke dauke da su.

Sashen dai ya nemi da kamfanin ya bude wayar mutumin nan wanda ya harbe mutane 14 har lahira, a San Bernardino, a watan Disamba, domin samun bayanai amma kamfanin yaki yarda.

Sai dai kuma bisa taimakon wani mutum, an ce an bude bayanan da ke kunshe, a wayar, ba tare da kutse ba.

A wata sanarwa da ya fitar, sashen ya ce bai kamata ma a shigar da karar ba tunda farko saboda masu amfani da wayar samfirin iPhone sun cancanci yin abubuwa a sirri.