Na fasa kwace shaidar 'yan ta'adda — Holland

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Salah AbdusSalam ake zargi da kai harin Paris a watan Nuwambar 2015
Shugaban kasar Faransa Francois Hollande, ya ce zai ajiye shirinsa na kwace takaddar 'yan kasa daga wadanda aka kama da laifukan ta'addanci.

Tunda farko an so a yi sauyin ne a kundin tsarin mulkin kasar lokacin da aka kai hare-haren Paris a watan Nuwamba.

Sai dai an samu rarrabuwar kai sosai a cikin jam'iyyar Mista Hollande, har hakan ta kai ga murabus din ministan shari'ar kasar.

Mista Hollande ya ce yanzu haka an ajiye batun bisa adawar da aka samu a majalisun dokokin kasar.

Wakilin BBC a Paris ya ce zazzafar adawar da aka samu a kan sauyin ya kasance wani abin kunya.

Karin bayani