Microsoft ya fitar da manhajar Bots

Hakkin mallakar hoto Getty

Kamfanin Microsoft ya fitar da wata manhaja da za ta iya aiki tamkar dan adam a madadin kamfanoni, kamar yadda Skype yake aiki.

Manhajar mai suna Bots tana aiki ne da kanta kuma ta na iya musayar sakonni kamar dai yadda dan adam ke yi.

Masu hulda da kamfanoni zasu iya amfani da Bots neman amsar tambayoyi da warware wasu matsaloli.

Shugaban kamfanin na Microsoft Satya Nadella ya ce, suna kokari ne su samar da wata manhaja da za ta yi aiki tamkar dai dan adam.

Kamfanin Microsoft dai ya na ta kokarin fadada ayukansa da bunkasa kasuwancinsa.