An rantsar da shugaban Myanmar

Image caption Sabon shugaban kasar Myanmar, Htin Kyaw yana shan rantsuwa.

Sabon shugaban kasar Myanmar, Htin Kyaw, ya karbi ragamar mulkin kasar, bayan shan rantsuwar kama aiki, a ranar Laraba.

Mista Kyaw ne shugaban mulkin farar hula na farko, a tsawon shekara 50, a kasar.

Htin Kyaw dai na hannun damar shugabar gwagwarmayar tabbatar da dimokradiyya ta kasar, Aung San Suu Kyi wadda tsarin mulki kasar ya haramtawa shugabancin Myanmar.

Tsohon Janar na soji, Thein Sein ne ya mika mulki ga Htin Kyaw.