Pakistan: Masu kishin Islama sun ki dakatar da bore

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Masu zanga-zangar sun kwashe kwanaki hudu suna yi.

<span >Masu kishin Islama da ke zanga-zanga a Islamabad babban birnin Pakistan, sun ce za su bijirewa umarnin hukumomi na kira kan dakatar da abin da suke yi din.

Suna bukatar a rataye wata mata kirista da aka kama da laifin yin sabo.

Masu zanga-zangar na kuma cike da haushin kashe wani mai gadi da aka yi a baya-bayan nan, sakamakon hallaka wani gwamnan yanki da ya yi.

Dakaru na cikin shirin ko-ta-kwana bayan ministan harkokin cikin gida na kasar ya yi barzanar bude wuta a wajen da masu zanga-zangar suka mamaye a ranar Lahadi.

Cikin kwanaki hudun da aka kwashe ana zanga-zangar dai yawan masu yi ya ragu daga kusan 10,000 zuwa 1,200 a yanzu.

Karin bayani