Somalia: Al-Shabab ta kai hari a hotel

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kasar Somaliya tana fama da mayakan Al-Shabab

Akalla mutane takwas ne suka rasa rayukansu, a wani tashin bam, a otal da ke birnin Galkayo na arewacin Somaliya.

Da safiyar ranar Alhamis ne aka ji karar tashin bam, a otal din, a inda rahotanni ke cewa harin kunar bakin-wake ne.

Magajin garin Gakayo, ya shaidawa BBC cewa an tabbatar da mutuwar mutane takwas, sai dai kuma ya ce adadin mamatan ka iya karuwa.

Birnin na Galkayo da ke yankin Puntland, yana da dan kwarkwaryar 'yancin kai kuma gwamnatin yankin tana fafatawa da kungiyar Al-Shabab wajen iko da yankin.

A baya-bayan nan ne yankin ya yi ikrarin fatattakar mayakan an Al-Shabab, to amma kuma kungiyar ta Al-Shaba ta dauki alhakin kai wannan harin.