Minista ta yi katobara kan suturar Musulunci

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Miss Laurence Rossignol na fuskantar barazanar yin murabus
Ministar hakkokin mata ta Faransa na fuskantar kiraye-kiraye kan bukatar ta yi murabus sakamakon kalaman da ta yi inda ta ce mata musulmai masu saka hijabi tamkar bakaken mata da suka amince da rayuwar bauta suke.

Laurence Rossignol ta yi wadannan kalamai ne a hirar da ta yi da wani gidan rediy, inda aka yi mata tambaya a kan kamfanonin suturu da suke kokarin tallata kasuwar suturun musulmai na hijabai da dogayen riguna.

Wata kungiyar Musulmai ta ce wannan abu da Miss Rossignol ta yi tamkar ta tofa kakaki ne kan tsarin mulkin Faransa da ba ruwansa da addini, kuma hakan zai taimaka ne kawai wajen karfafa gwiwar masu sanya mutane a kungiyar IS mai ikirarin jihadi.

Kazalika, wani dan kasuwa Pierre Berge, ya koka kan kokarin da kamfanoni suke don tallata suturun musulmai, yana mai cewa kamata ya kamfanonin su mayar da hankali kan inganta kwalliyar mata, ba hada kai da masu kokarin boye adon matansu ba.

Karin bayani