Ruftowar gada ta hallaka mutane 14 a India

Hakkin mallakar hoto
Image caption Rushewar gadar ya hallaka mutane 14
>Ma'aikatan ceto a birnin Kolkata na Kasar Indiya na amfani da hannayensu da kuma diga wajen kokarin ceto mutanen da wata gadar sama ta ruftawa, da suka hada da wasu fasinjojin wata karamar motar safa.

'Yan sanda sun ce a kalla mutane 14 ne suka mutu a lokacin da gadar wacce ake kan ginata, ta ruguzo.

An shiga yanayi na rudani yayin da sojoji da kuma 'yan sanda suke korar mutanen da suke kokarin gano 'yan uwansu.

Rahotanni sun ce an ceto a kalla mutane 15 da suka ji munanan raunuka.

Image caption Ga taswirar gadar da ta rufto a Kolkata

Amma wani wakilin BBC da ke wajen ya ce manyan motoci ba sa iya karasawa wajen da lamarin ya auku saboda titunan a matse suke sosai.

Karin bayani