Kenya: An karrama wanda ya bai wa kiristoci kariya

Hakkin mallakar hoto PSCU Kenya
Image caption Shugaba Kenyatta ne ya bayar da lambar yabon
Kasar Kenya ta bayar da lambar yabo mafi girma ta jarumta ga Malamin nan Musulmi wanda aka kashe shi sakamakon bai wa kiristoci garkuwa, lokacin da mayakan al-Shabab suka kai wa motar bas din da suke ciki hari.

Labarin abin da ya faru din ya mamaye kafafen yada labarai na duniya a watan Disambar 2015.

Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta ne ya sanar da bayar da lambar yabon a jawaboin da ya gabatar wa 'yan kasar.

Salah Farah na cikin mota kirar basa ne a kan hanyarsa ta zuwa Mandera a lokacin da mayakan suka tare motar a watan Disamba.

Mayakan sun umarci Musulmai da Kiristoci da su ware kansu, amma sai Farah na daga cikin Musulman da suka ki bin umarnin.

Harsashi ya samu Mista Farah wanda ya mutu bayan da ya shafe wata guda yana jinyar raunin.

Karin bayani