Zaha Hadid fitacciyar mai zane ta mutu

Hakkin mallakar hoto RIBA l PA
Image caption Zaha Hadid, ita ce mace ta farko cikin masu zane-zane da ta samu kyautar zinariya ta sarauniya.

Zaha Hadid, hafaffiyyar 'yar Irakin nan mai aikin zane-zanen gidaje ta rasu tana da shekaru 65.

Zaha wadda shahararriyar mai zane-zane ce da ta yi fice sosai ta, gamu da ciwon murar fuka, watau Bronchitis a farkon makon nan, kuma a karshe zuciyarta ta buga a asibitin da take jinya a birnin Miami na Amurka.

Zaha wacce mazauniyar Ingila ce, ta yi zanen manyan gine-gine a duniya, wadanda suka hada da ginin taron mawaka watau Guangzhou Opera House da ke China, da ginin wasanni na London Aquatics Center, inda aka gudanar da wasannin Olympic na shekarar 2012.

BBC ta bayyana zane-zanen Zaha da cewar suna da kwalisa na zamani da ban sha'awa.

Ba a jima da yi mata kyautar gwanaye ba, inda aka bata zinariya, watau Royal Gold Medal, a matsayin mace ta farko cikin masu zane-zane da ta taba samun irin wannan kyautar.