Afrika Ta Kudu: Akwai yiwuwar tsige Zuma

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wannan ne gidan da yake cigaba da janyo cece-kuce.

Jam'iyyar Adawa ta Democratic Alliance, a Afirka ta Kudu ta ce shugaban kasar, Jacob Zuma ka iya fuskantar tsigewa daga kan mulki bisa tuhume-tuhumen rashawa da cin hanci.

Da safiyar Alhamis ne dai babbar kotun kasar ta zartar da cewa shugaba Jacob Zuma ya karya ka'ida saboda kin biyan gwamnati kudin da ya yi amfani da su wajen yi wa gidansa kwaskwarima.

Jam'iyyun adawa guda biyu ne dai suka shigar da karar, a inda suka nemi a hukunta shugaban bisa yin amfani da kudaden gwamnati wajen gyaran gidansa, a kauyen Nkandla.

An kashe dala miliyan 23 kudi wajen kwaskwarimar da sunan tsara gidan domin ya dace da tsarin samar da tsaro. Gyare-gyaren ya kunshi tafkin wanka na zamani da filin taro da kuma garken shanu.

Kotun dai ta umarci zuma da ya mayar da wani kaso na kudaden zuwa baitil mali.

A wani jawabi da ta yi, bayan zartar da hukuncin, jam'iyyar ta Democratic Alliance ta ce Zuma ya aikata laifukan da za su sanya a tsige shi.