Ko ka san illar ƙiba?

Hakkin mallakar hoto AP

Wani sabon rahoto yace, yawan masu ƙiba na karuwa a duk faƙin duniya, kuma da wuya a cimma ƙoƙarin rage ƙiba.

Masana kimiyya da suka yi wani rubutu a mujallar kiwon lafiya ta Birtaniya, wato Lancet sun ce, shekaru 40 da suka gabata rashin ƙiba shi ne babbar matsala, amma a yanzu yawan ƙiba shi ne babban ƙalubale a duk duniya.

Rahoton ya kuma ce, yawan maza dake da mummunar ƙiba ya nunka na mata.

Masana kimiyyar sun ce, ba za a iya warware wannan matsala ta ƙiba ba ta hanyar kiwon lafiya, ko kuma samar da hanyoyin motsa jiki.

Masanan sun yi amfani da bayanai da suka tattaro daga ƙasashe fiye da 180 yayin wannan bincike.