Zanga-zanga a Brazil kan tsige Rouseff

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Masu zanga-zangar dai suna son hana tsige shugaba Delma Roussef.

Dubban magoya bayan shugabar Brazil Dilma Rouseff ne suka yi wata zanga-zanga, a birane kusan talatin domin nuna adawa da yunkurin tsigeta.

Zanga-zangar dai tamkar martani ne da shugabar ke mayarwa abokan hamayyarta, bayan zargin cin hanci da rashawa da ya dabaibaye gwamninta.

Ana kuma binciken tshohon shugaban kasar kuma makusancin Dilma, Lula da Silva, bisa zarge-zargen cin hanci, zargin da ya musanta.

Sai dai kuma Lula yana zargin alkalin da ke jagorantar binciken nasa da cewa yana hakonsa ne.

Yanzu dai, kotun kolin kasar ta karbe shari'ar daga hannun alkalin da ake zargi da nuna karan tsana.