SHIRIN SANIN KAI 2016: Tseren rakuma; kasuwanci mai kawo miliyoyi

Hakkin mallakar hoto Other
A dakin da matafiya ke jiran jirgin da zai tashi daga babban filin jirgin sama na Dubai zuwa birnin Doha na Qatar, wasu maza ne biyu ke zaune cikin shigar Larabawan yankin Gulf, kai da ganin rawaninsu za ka gane cewa daga kasar Oman suke, duk da dai ba kowa ne zai gane hakan ba sai wanda ya san al'adun mutanen yankin.

Da na fara takalarsu da zance, sai ga Faisal da Ahmad na gaya min dalilin ziyarar da suka kawo Dubai, wanda ya hada da halartar tseren rakuma.

Tseren rakuma? Tambayar da na nanata kenan, ina mai ɗokin son jin labarin.

Karaf sai Faisal ya amsa min da cewa, ''Ina matukar son kiwon rakuma da kuma tserensu, al'adar zuri'armu ce.''

Ya kara da cewa, ''Kakana na wajen uba da zuri'arsa suna son kiwon rakuma, shi kuma kakana na wajen uwa da tasa zuri'ar suna son kiwon dawakai. Tun ina yaro nake son rakuma.

Hakkin mallakar hoto Other
Image caption Faisal ya ce son rakuma a jininsa yake
''Kwalam da makulashe''
Hakkin mallakar hoto Other

Duk da cewa Faisal na aiki da kamfanin sadarwa, to ba ya ga aikin nasa yana kuma kiwon rakuma da taimakon iyalansa saboda a cewarsa, ''Hakan yana rage wahalhalun wajen aiki da muka yi na tsawon mako.''

A wannan zamanin ana kiwon rakuma ne ba wai don samun nononsu da nama ba kawai kamar yadda aka saba, a maimakon haka yanzu ana amfani da su ne don samun miliyoyin kudi.

Faisal ya bayyana min cewa ana ciyar da rakuma abinci mai inganci da suka hada da zuma da madara da kwai da dabino da sauran sinadaran bitamins.

Sai na yi maza na tambaye shi, ''Ku ciyar da rakumi wadannan kayan kwalam har da zuma, hakan bai yi tsada ba?''

''Muna kashe fam 1,000 duk wata domin shirin sanya rakumi a gasar tsere.'' Wannan ce amsar da Faisal ya bani.

Faisal ya kuma shaida min cewa shekarun da rakumi kan fara shiga gasar tsere ya danganta daga shekara biyu zuwa bakwai, da zarar dai mai bayar da horo ya ga cewa rakumin ya shirya.

Dole ne a ce tseren rakumi abu ne mai tsada. Shugabannin kasashen yankin Gulf ne yawanci suke kayyade farashin rakuma.

Faisal ya ci gaba da cewa, ''Suna sayen rakuma daga masu shi su kuma kiwata su, amma basa taɓa sayar da su. Masu mulki kan tsaya a matsayi ɗaya da talakawansu a yayin shiga gasar.''

Ya kara da cewa, ''Suna yin hakan da taimakon mutanen Oman wadanda suka san ciki da bai na tseren rakuma.''

''Farashin rakuma''

Amma farashin rakumi kan kai nawa? Faisal ya ce farashin rakumi na farawa daga kusan dala 55,000 amma farashin kosassu sosai kan haura haka. A shekarar 2010 wani dan kasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa mai son tseren rakuma ya kashe fam miliayn 6.5 a kan rakuma uku.

Kyaututtukan da ake bayarwa na lashe gasar tseren rakuma na da yawa sosai, daga tsakanin dala miliyan biyar zuwa dala miliyan 10, amma wasu kan samu har dala miliyan 30.

Ba abin da ya sha wa Faisal kai a lokacin da yake yi min bayanin wadannan makudan kudade, ni kuwa ya bar ni ina kakabi amma kuma bana so ya gano ni.

Amma fa kai wa ga wannan mataki ba abu ne mai sauki ba, dole ne sai rakuman sun tsallake wasu zagaye na gwaji a kasashen yankin Gulf, inda za a bai wa wadanda suka yi nasara damar wucewa zagaye na gaba.

Yawan nanata muhimmanci tseren rakuma da Faisal ke yi min ya sa na ƙara gane rawar da ƙasashen yankin Gulf suke da ita a kasuwannin rakuma, su kan sayar da wasu dabbobin su kuma shigar da wasu gasar tsere.

Ana yin gasar tseren rakuma a kasa-kasa kowanne mako don a samu damar zabo wadanda za su fi yin abin kirki idan aka zo babbar gasar, kamar, ''Gasar cin kofin yankin Gulf'', da Gasar shekara-shekara ta Dubai da kuma Gasar tseren rakuma ta Qatar.

''Makudan kudi''
Hakkin mallakar hoto Other

Tsawon gudun da rakuman ke yi na tsakanin kilomita daya da rabi zuwa kilomita takwas, ya danganta da shekarun rakuma, da na 'yan shekara biyu da hudu da shida da kuma na 'yan shekara takwas.

Duk rakumin da ya yi nasarar lashe gasar, zai samu kyautar karramawa ta takobi da ke nuni da hakan, da kuma tsabar kudi dala miliyan uku. ''Tamkar dai gasar tsalle-tsalle ta Wembley,'' in ji Faisal.

Sai dai tambayar da nayi wa Faisal ita ce, ''Ganin irin wannan makudan kudi da ake kashewa a tseren rakuma, mutane suna saka caca kuwa?''

Amsar da ya bani ita ce, ''Sam ba a haka, don kuwa haramun ne a Musulunci.''

A shekarun baya-bayan nan kasashen yankin Gulf sun daina amfani da yara wajen hawan rakuma, a maimakon haka sai suke amfani da butum-butumi bayan sukar da suka yi ta sha daga kungiyoyin kare hakkin dan adam na duniya, wadanda suka ce yara na mutuwa sakamakon tseren rakuman da ake sa su yi.

Amma manyan har yanzu suna hawa tseren rakuman in ji Faisal, wanda shi ma ya yi amanna cewa wannan tseren rakuma na iya zama wani shahararren wasa a bangarori daban-daban na duniya, har da Turai.

Amma sai na tambaye shi cewa baya ganin sanyi ya yi yawa a Turai? Sai Faisal ya café da cewa, ''Ai su rakuma sun fi son haka ma, saboda yanayin zafi da rana kan rage wa rakuma kuzari.

Tseren rakuma a Turai? Wa ya sani ko hakan ya faru nan gaba.