Za a rantsar da shugaban Niger

Nan gaba a yau ne ake sa ran shugaban Nijar Mahamadou Issoufou zai yi rantsuwar soma sabon wa'adin mulki na shekaru biyar.

Shugaba Issoufou zai yi rantsuwar soma sabon wa'adin mulkin nan gaba a yau a birnin Yamai inda za a yi bukukuwa.

Cikin makon jiya ne hukumar zabe CENI ce ta bayyana shugaba Muhammadou Issoufou a matsayin wanda ya lashe zaben kasar.

Sai dai gamayyar jam'iyyun adawa dake goyon bayan Hama Amadou sun yi watsi da zaben da ya baiwa shugaba Issoufou nasara.

Wannan zai kasance wa'adin mulki na biyu kenan da shugaba Issoufou zai yi.

Nijar dai tana fuskantar kalubala tattalin arziki, siyasa da kuma tsaro.