North Korea ta sake gwajin makami mai linzami

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kasashen Amurka da China sun gargadi kasar da ta daina amfani da makamin nukiliya.

Kasar Korea ta Arewa ta sake gwajin makami mai linzami, 'yan sa'o'i bayan da shugabannin China da Amurka, suka yi kira ga kasar, da ta sauya aniyarta ta amfani da makamin mai linzami.

Korea ta Kudu dai ta ce Korea ta Arewa ta harba mata makami mai linzami daga gabashin gabar ruwan kasar zuwa cikin teku.

Shugabannin kasashe da dama ne dai suke halartar wani taron koli, a kan makamin nukiliya, da ake gudanarwa, a Washington.

Shugaba Obama ya ce shi da shugaban China, Xi Jinping sun kudiri aniyar ganin yankin na Korea bai fuskanci barazanar makamin nukiliya ba.

Shi kuma mista Xi ya nemi kasashen da su aiwatar da takunkumin Majalisar Dinkin Duniya, a kan Korea ta Arewa.