Mata masu sana'ar bumburutu

Maza aka fi sani da wannan sana'a ta bumburutu a bakin titi, inda suke dauke da jarkoki suna sayar da man fetur, idan babu a gidajen mai.

Harka ce ta neman kudi da yanzu ma ta samu shiga a wajen mata, wadanda a da ke tallan gyada da ayaba, a yanzu suma sun shiga sayar da man fetur:

Ana zargin wadanda ke shigowa da man fetur din da hannu a karancinsa, inda a hukumance ake sayar da shi naira 86, amma a lokacin wannan karanci da ake ciki ana sayar da shi har naira 250.

An soma karancin man tun watan Janairu, amma al'amarin ya ta'azzara a makon da ya gabata, lokacin da Ministan man ya sanar da cewa lamarin zai iya kai wa har watan Mayu.

Harkar bumburutu na kawo riba sosai cikin dan kankanin lokaci.

A baya, Mary (wace aka nuno a kasa) ta shekara biyar tana tallar ayyaba da gyada a birnin Abuja.

Ribar da ta ke samu karshen kowace rana bai tafi naira 1400 ba.

Amma tun a makon da ya gabata da ta koma harkar bumburutu, ta ce tana jin dadin inda iskar ta dosa:

Matan sun ce suna bai wa ma'aikatan gidajen man cin hanci domin su sayar masu da man fetur din.

Kasuwar man na ci sosai saboda yadda jama'a ke dogara da shi domin gudanar da ayyukansu wajen amfani injin din da ke samar da wuta.